NAFDAC ta dakatar da anfani da sabulun wanka na Dove
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna NAFDAC ta dakatar da amfani da wani sabulun wanka na Dove Beauty Cream (100g) mai lamba 81832M 08 da aka samar a kasar Jamus.
“Sabulun bai bi ƙa’idar Samar da Kayayyakin Kwalliya ba kamar yadda aka ce yana dauke da sinadarin Butylphenyl Methylpropional (BMHCA), wanda aka haramta saka shi a cikin kayan kwalliya saboda hadarinsa ga tsarin halittun haihuwa,” in ji NAFDAC a cikin wata sanarwa ranar Litinin.
NAFDAC ta kuma yi gargaɗi a kan amfani da kayan kwalliyar da ba a yi wa rajista ba waɗanda aka yi wa kiranye ko aka haramta a sauran ƙasashe saboda suna ɗauke da sinadarin MBHCA.
KU KUMA KARANTA: NAFDAC ta rufe shaguna 100 A Enugu
Hukumar ta nemi masu shigar da kayayyaki da sayar da su da kuma masu samar da kayayyakin kula d alafiya da su saka ido sosai a harkar samar da kaya don guje wa shigar da duk wani abu marar kyau ko marar rajista ko kuma kayayyakin kula da lafiya marasa inganci.
Sanarwar NAFDAC ta jaddada cewa wasu ƙasashen a Ƙungiyar Tarayyar Turai sun dakatar da amfani da duk wasu kaya na Dove saboda dalilai na rashin inganci.