NAFDAC ta buƙaci a zartar da hukuncin kisa kan masu fataucin ƙwaya
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta ba da shawarar zartar da hukuncin kisa akan masu fataucin ƙwaya.
A cewar babbar daraktar hukumar, Mojisola Adeyeye, tsattsauran hukunci ne kawai zai dakatar da fataken kwaya musamman ma yadda take sanadiyar mutuwar kananan yara.
KU KUMA KARANTA:NAFDAC ta lalata kayayyakin jabu na Naira biliyan 1.3 a Abuja
Shugabar hukumar ta NAFDAC ta kuma nemi hadin kan bangaren shari’a da majalisar kasa wajen ganin wannan buri ya zama gaskiya.
A cewarta, a shirye hukumar take ta yi hadin gwiwa da ‘yan majalisa da sauran masu ruwa da tsaki a kan batun, inda Adeyeye ta koka da karancin ma’aikata a hukumar.
Ta yi amannar cewar da ma’aikata kimanin 2, 000 a fadin Najeriya da karancin kudade, babu yadda za’a yi NAFDAC ta gudanar da ayyukanta yadda ya dace.