NAFDAC ta ƙona ƙwayoyin tramadol dubu 491 da aka kama a Kano

0
216
NAFDAC ta ƙona ƙwayoyin tramadol dubu 491 da aka kama a Kano
Ƙwayoyin Tramadol da aka ƙona

NAFDAC ta ƙona ƙwayoyin tramadol dubu 491 da aka kama a Kano

Daga Jameel Lawan Yakasai

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta ƙasa (NAFDAC) ta ƙone ƙwayoyin Tramadol 225mg guda 491,000 da aka kama a Kano.

Wannan na cikin sanarwar da Daraktan Bincike na NAFDAC, Dr. Martins Iluyomade, ya gabatar a madadin Shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye.

Sanarwar ta ce Hukumar Kwastam shiyyar Kano da Jigawa ce ta kama kayan a ranar 28 ga Mayu, 2025, karkashin jagorancin Kwanturola Dalhatu Abubakar, bayan wasu bata-gari sun shigo da su daga Jamhuriyar Nijar.

KU KUMA KARANTA: Hukumar Kwastam da NAFDAC sun kama miyagun ƙwayoyi da kuɗinsu ya haura Miliyan 150

NAFDAC ta ce ƙwayoyin sun kai adadin 491,000 kacal, da darajarsu ta kai naira miliyan 91.

Farfesa Adeyeye ta bayyana wannan a matsayin babbar nasara ta haɗin gwiwar hukumomi wajen yaki da safarar miyagun kwayoyi a ƙasar.

Ta kuma bukaci jama’a da su ci gaba da bayar da rahoton duk wani motsi na safarar miyagun ƙwayoyi domin hukumar ta ɗauki matakin gaggawa.

A nasa ɓangaren, mataimakin Kwanturola na sashen aiwatar da hukunci na Kwastan a shiyyar Kano da Jigawa, Yusuf Idris, ya ce an kama Tramadol ɗin ne a kan iyakar Mai Gatari da ke tsakanin Najeriya da Nijar.

Leave a Reply