Na zaɓi na cire tallafin man fetur a ranar farko duk da babu shi a jawabina – Tinubu

1
409

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce shi da kansa ya zaɓi ya bayyana cire tallafin man fetur a ranar farko da ya zama shugaban ƙasa duk da cewa ba a rubuta shi ba a cikin jawabin da ya gabatar.

Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da ‘yan Najeriya mazauna Faransa ranar Juma’a, kamar yadda mai ba shi shawara kan ayyuka na musamman Dele Alake ya faɗa cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta ce: “Tinubu ya yi bayani cewa mai ba shi shawara kan harkokin kuɗi Wale Edun, da mai ba shi shawara kan ayyuka na musamman Dele Alake ba su saka maganar cire tallafi ba a jawabinsa, amma ya ji cewa ya kamata ya kawo ƙarshensa a ranar farko.”

Shugaban ya kuma bayyana tallafin a matsayin “zamba” da ke “hana cigaba” yayin ganawar tasa da ‘yan Najeriya.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya ba da umarnin mayar da NEMA, NAHCON ƙarƙashin ofishin mataimakin shugaban ƙasa

Tun daga ranar 29 ga watan Mayu da Tinubu ya sanar da cewa “tallafin man fetur ya tafi” farashin man ya ninninka, inda ake sayar da lita ɗaya kan Naira ɗari 540 zuwa sama saɓanin N195 da aka saba sayarwa.

1 COMMENT

Leave a Reply