Na sha baƙar azaba a hannun masu garkuwa da mutane – ɗalibar Ondo da aka ceto

Wata ɗalibar kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Ondo, Rufus Giwa Polytechnic, Owo, Odey Olayemi, ta bayyana irin halin da take ciki a wurin masu garkuwa da mutane bayan ta shafe kwanaki bakwai a hannunsu.

Ode mai shekaru 23 ta zanta da manema labarai a ofishin hukumar tsaro ta jihar Ondo (Amotekun) da ke Akure bayan an biya kuɗin fansa Naira 350,000 domin a sako ta daga hannun waɗanda suka sace ta.

Ɗalibar wadda ta bayyana cewa an sace ta ne yayin da take kan hanyarta ta zuwa gona a ƙauyen Ago-Oyinbo da ke ƙaramar hukumar Akure ta Arewa, ta ce ta sha baƙar azaba a hannun waɗanda suka sace ta.

Ta ce, “Na kasance a ƙauye ne don in taimaka wa ’yan uwana mata kafin ranar da za a koma makaranta don samun wasu kuɗaɗe a dawo da su makaranta, amma a ranar muna cikin gona sai muka ga mutune uku suna kan hanyarmu.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan sanda sun ceto mutane huɗu da aka yi garkuwa da su a Kwara

“Na gaya wa ’yan’uwana cewa zan gudu amma sun ce kada in je ko’ina kuma ba za su yi komai ba.

Da suka zo wurinmu, suka ce mu durƙusa, muka yi musu biyayya. “A lokacin ne muka fara roƙonsu.

Biyu daga cikinsu na ɗauke da bindigogi, na ukun kuma yana ɗauke da kwalabe.

Sai suka ce in daina bin su, sai suka ɗauki sandar rogo suka fara dukana.”

Odey ta ce masu garkuwa da mutanen sun yi mata barazanar cewa za su kashe ta idan har ta ƙi ba su haɗin kai wajen neman kuɗin fansa.

Ta ba da labarin cewa na yi kwana bakwai tare da su kuma sun nemi lambar wayar babana amma ban san lambar a kai na ba.

Na rasa me nake tunani saboda tashin hankali. “Amma da na ba su lambata, sai suka fara ƙiran wayata.

Wayar an ƙira, ta yi ta ƙara amma ba wanda ya ɗauka. Daga baya, wata ’yar’uwata da ta zo daga Akure zuwa ƙauyenmu ta ɗauki waya kuma aka gaya mata cewa an sace ni kuma ina tare da su.

“Yar uwata ce ta je bayar da rahoto kafin Amotekun ya fara aiki sannan al’ummar garin suka tara Naira 350,000 kafin a sako ni sakamakon farautar da jami’an tsaro suka yi.

Tun da farko, kwamandan Amotekun a jihar, Mista Adetunji Adeleye, ya ce jami’an hukumar sun yi nasarar ceto wanda abin ya shafa bayan sun yi farauta.

Mista Adeleye ya ce sai da jami’ansa suka tsallaka rafi ta cikin dajin domin kamo waɗanda ake zargin, sannan kuma an ƙubutar da wasu da masu garkuwa da mutane suka yi garkuwa da su.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *