Na gaya wa Shugaban Ƙasa matsalolin Zamfara kuma ya ba ni tabbacin kawo ɗauki – Dauda Lawal

0
170

Gwamnan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya Dauda Lawal Dare ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ba shi tabbacin kai wa jihar tasa ɗauki, wacce ke fama da tarin matsalolin tsaro.

An shafe shekaru ana fama da matsalar ƴan bindga da masu satar mutane don karɓar kudin fansa a Zamfara, inda a wasu lokutan har suke tayar da garuruwa da ƙauyuka ta hanyar fattakar mazauna wajen da ƙone-ƙone.

A wani saƙon bidiyo da Fadar Shugaban Ƙasar ta aike wa manema labarai, Gwamna Lawal ya ce ya gana da Shugaba Tinubu ne a jiya Talata a fadarsa da ke Abuja, “kuma ganawar ta yi amfani ƙwarai da gaske.”

“Jama’a yau a matsayina na gwamnan Zamfara na zo fadar Shugaban Ƙasa na gan shi don na fada masa irin matsalolin rashin tsaro da muke fuskanta a Zamfara, kuma tattaunawar ta yi amfani ƙwarai da gaske don ya ba ni tabbacin cewa da ikon Allah zai yi duk abin da zai yi don a samu sauƙi a jihar,” in ji gwamnan.

KU KUMA KARANTA: Jami’an tsaro sun gayyaci Sheikh Gumi — Gwamnati

Ya ce kusan duka matsalolin da ake fama da su a sauran yankunan arewa suna farowa ne daga jihar Zamfara, don haka idan har aka magance rashin tsaro a can, to sauran wuraren ma za su samu sauƙi.

Jihohin Katsina da Sokoto da Neja da Kaduna na daga cikin manya da ke fama da rashin tsaro, baya ga Zamfara, inda har makarantu ake shiga ana kwashe ɗalibai da kuma kashe rayuka da sace mutane.

Gwamnan ya ƙara da cewa “Idan muka yi ƙoƙari aka yi wani abu wanda zai kawo sauki to kusan duk arewacin Najeriya in shaa Allah za mu samu sauki.

“Na ji daɗin tattaunawar kuma na yi farin ciki, kuma Shugaban Ƙasa ya gamsu da duk bayanin da na yi masa kan matsalolin da muke fuskanta a Zamfara na maganar tsaro.

“Wadansu da da bai ma sani ba amma yau ya san kusan komai da ke faruwa a wannan jiha tamu,” a cewar Gwamnan.

Leave a Reply