Naɗin Shugaban NIPOST: Wasu daga cikin ma’aikatan, sun yi zanga-zangar ƙin amincewa da naɗin

0
197

Ma’aikatan aikewa da saƙonni ta Nijeriya (NIPOST), sun rufe babban ofishin hukumar da ke Abuja, suna zanga-zangar nuna adawa da naɗin Tola Odeyemi a matsayin babban jami’in gudanarwa a hukumar.

Ajuri Ngelale, mai magana da yawun shugaban ƙasa, ya bayyana a makon da ya gabata cewa, shugaban ƙasa Bola Tinubu, ya yi wasu sauye-sauye a shugabancin hukumomin sadarwa da suka haɗa da NIPOST.

Sai dai jim kaɗan bayan da labarin naɗin Odeyemi ya ɓulla, an samu rahotannin cewa an mayar da Adeyemi Adepoju, wanda aka kora daga muƙamin babban jami’in gudanarwar hukumar.

A cikin wani faifan bidiyo, an ga Adepoju yana jawabi ga wasu ma’aikata da suka yi iƙirarin cewa Tinubu ya sake naɗa shi.

KU KUMA KARANTA: Tinubu ya naɗa jigon ɗan PDP a matsayin shugaban FERMA

Sai dai a ranar Litinin ma’aikatan sun yi zanga-zangar sun kuma hana sabuwar shugabar hukumar ta NIPOST shiga ofishin hukumar, inda suka ce naɗin nata ya saɓa wa muradinsu.

Ma’aikatan, waɗanda suka ce sun fi son Adepoju, sun rera waƙoƙin haɗin kai, ɗauke da allunan nuna rashin amincewa da sabon naɗin.

Leave a Reply