Muƙarraban Ganduje sun mayar da martani kan kwamitin da Gwamnan Kano ya kafa na binciken tsohon gwamnan

0
189

Muƙarraban tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, sun mayar da martani ga yunƙurin gwamnatin jihar mai ci, ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar NNPP, na kafa kwamitocin bincike da kuma gurfanar da tsohon gwamnan a gaban babbar kotun jihar kan tuhumar badaƙalar wasu kuɗaɗe.
Sai dai masana sun ce matakin zai kawar da hankalin gwamnatin daga muhimman buƙatun Jama’a.

A jiya ne gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya kafa wasu kwamitoci guda biyu da aka ɗorawa nauyin bincikar yadda gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta sarrafa kadarorin gwamnatin cikin shekaru 8 da suka shuɗe, da kuma yadda aka samu tarzomar siyasa dama ɓatan yara a wasu sassan jihar a lokacin gwamnatin ta Ganduje.

Kazalika, gwamna Abba Kabir Yusuf ya gurfanar da tsohon gwamna Abdullahi Umar Ganduje a gaban babbar kotun jihar bisa zargin rashawa da cin hanci na maƙudan miliyoyin naira da kuɗaɗen ƙetare na dala.

Barrister Haruna Isa Dederi shi ne kwamishinan shari’a kuma babban Atoni na jihar ta Kano ya yi ƙarin bayani dangane da wannan mataki na gwamnati, “tun ranar da aka rantsar da mai girma gwamna, ya faɗa a gaban jama’a cewa, ya tarar da abubuwa marasa daɗi waɗanda suka shafi badaƙalar da haƙƙoƙin jama’a, kuma zai bi sawu domin ya binciko abin da yake na al’umma ne, don haka ba bita da ƙulli ba ne batu ne da ya shafi nauyi daya rataya a wuyan gwamnati.”

Sai dai a martaninsa ga wannan yunƙuri, Abdullahi Umar Ganduje tsohon gwamnan Kano kuma shugaban Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ya bayyana matakin da cewa, gwamnan na Kano ne ke ƙoƙarin lullube gazawar sa a fagen shugabanci, domin kuwa duk da maƙudan biliyoyin Naira da gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu ke turawa jihar Kano a kowane wata, har yanzu gwamnatin ta Abba Kabir Yusuf ba ta taɓuka wa Kanawa komai ba tsawon shekara guda da kama madafan iko.

KU KUMA KARANTA:Gwamna Abba ya ƙaddamar da kwamitocin bincike kan rikicin siyasa da ta’annati da dukiyar Kano

A cikin wata sanarwa da sakataren labarun shugaban na APC Mista Edwin Olofu ya fitar, yace jahiltar tsarin doka da oda ta fuskar tafikar ayyukan gwamnati ne ya sanya Gwamna Abba Kabir Yusuf gurnafar da tsohon gwamna Ganduje a gaban kotu da irin waɗannan tuhume-tuhume.

Shi-ma Dakta Musa Iliyasu Kwankwaso, tsohon kwamishinan raya karkara a gwamnatin gwamna Ganduje yace, “wannan ba wani abu ne sabo ba a wurin ‘yan siyasa, ballantana a zo ana cece-kuce. Mu abin da ya dame mu a yanzu shi ne mutane suna cikin hali na yunwa, kamata ya yi a fito a taimaki mutane, ba wannan labarin ake nema ba, kayayyaki da kuɗaɗen da gwamnatin tarayya ta Jam’iyyar APC ta turo Kano a taimaki al’umma shi ne abin da ya damu mutanen Kano dana ƙasa baki ɗaya.”

Sai dai masana harkokin siyasa da lamuran mulki sun fara fashin baƙi.

Dakta Sa’idu Ahamd Dukawa Malami ne a jami’ar Bayero Kano na cewa, “komai daɗewa, ya kamata idan mutum ya yi laifi, ya girbi abin da ya shuka, don haka a bincika laifukan da gwamnatin da ta wuce ta yi, a ɗauki mataki hukunci ba laifi ba ne, amma inda gizo yake saƙa shi ne idan za’a tuhumi gwamnatin da ta shuɗe, sai an yi da ikilasi, ya zama gwamnatin da take tuhumar wadda ta gabace ta ba ta irin aikin ko laifin da take tuhuma an aikata a baya.”

Leave a Reply