Mutum 9 sun mutu, sama da 2,700 sun ji rauni sakamakon bindigar na’urori

0
76
Mutum 9 sun mutu, sama da 2,700 sun ji rauni sakamakon bindigar na'urori

Mutum 9 sun mutu, sama da 2,700 sun ji rauni sakamakon bindigar na’urori

Aƙalla mutum tara ne suka mutu sannan wasu sama da 2,750 da suka haɗa da mayakan Hizbullah da likitoci, suka jikkata, a lokacin da na’urorinsu na yaɗa labarai suka fashe a faɗin ƙasar Lebanon, kamar yadda kafafen yaɗa labarai da jami’an tsaro suka bayyana.

Wani jami’in ƙungiyar Hizbullah da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Associated Press cewa, ‘yan ƙungiyar sun samu raunuka a sassa daban-daban na kasar Labanon da Syria, a lokacin da wasu na’urorinsu na hannu suka fashe a ranar Talata.

Jami’in ya zargi Isra’ila da tayar da na’urorin, inda ya ƙara da cewa, wannan shi ne “taɓarɓarewar tsaro mafi girma” da ƙungiyar ta fuskanta a yakin kusan shekara guda da Tel Aviv.

Wasu majiyoyin tsaro biyu sun shaida wa kamfanin dilancin labaran Reuters cewa mayaƙan Hizbullah biyu da suka haɗa da ɗan majalisar dokokin Hizbullah ne suka mutu sakamakon fashe-fashen.

Bugu da ƙari, an kuma kashe wata ƙaramar yarinya a yankin Baalbek da ke arewa maso gabashin kasar Lebanon, a cewar kafofin yada labaran Lebanon.

KU KUMA KARANTA: Trump na zargin Kamala Haris da ƙin jinin Isra’ila

Rahotannin sun bayyana sunanta da Fatima Jaafar Abdullah ‘yar shekara 9 ‘yar wani ɗan Hizbullah.

Kazalika, jakadan Iran a birnin Beirut ya samu rauni sakamakon fashewar wani abu amma raunin da ya samu bai yi tsanani ba, kamar yadda kafafen yaɗa labaran ƙasar suka ruwaito.

“Jakadan Iran a Lebanon Mojtaba Amani ya samu rauni sakamakon fashewar wani abu,” in ji gidan talabijin na ƙasar, ya ƙara da cewa “yana cikin hayyacinsa kuma ba ya cikin wani haɗari.”

A nata ɓangaren ma’aikatar lafiya ta ƙasar Lebanon ta buƙaci dukkan ‘yan ƙasar da suka mallaki na’urorin sadarwa na pager da su yi gaggawar kawar da su.

Wannan lamari dai shi ne irinsa na farko tun bayan da Isra’ila da kungiyar Hizbullah suka fara musayar wuta a kullum bayan da Tel Aviv ta ƙaddamar da yakin Gaza a watan Oktoban bara.

‘Yan jarida da masu ɗaukar hoto a kudancin birnin Beirut sun ga motocin ɗaukar marasa lafiya suna garzayawa da waɗanda suka jikkata zuwa asibitocin yankin.

Kungiyar agaji ta Red Cross ta kasar Lebanon ta ce karin motocin daukar marasa lafiya 50 da ƙwararrun likitocin gaggawa 300 na cikin shirin ko-ta-kwana domin kai ɗaukin waɗanda lamarin ya rutsa da su sakamakon fashewar bututun mai.

Wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP a Gabashin Labanon ya ce an jikkata wasu da dama a irin wannan lamari a yankin kwarin Bekaa na ƙungiyar.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Labanon ya ba da rahoton “wani lamari na tsaro da ba a taba ganin irinsa ba” game da “na’urorin hannu” sun tashi a yankuna da dama.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya rawaito jami’an tsaro cewa waɗannan na’urori na pagers da suka tarwatse na daga cikin irin na baya-bayan nan da ƙungiyar Hizbullah ta samu a watannin baya.

Ƙungiyar Hizbullah ta buƙaci mambobinta da su guji amfani da wayoyin hannu bayan yaƙin da Isra’ila ke yi a Gaza ya fara kauce wa keta fasaha.

‘Yan Hizbullah suna sadarwa ta hanyar tsarin sadarwarsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here