Mutum 6 sun mutu sakamakon hatsarin mota a Zamfara 

Hukumar Kiyaye Haɗura ta Ƙasa (FRSC) a Jihar Zamfara ta tabbatar da mutuwar mutum shida a Gusau, sakamakon wani hatsarin mota.

Kwamandan hukumar a jihar, Iro Danladi, ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a Gusau a ranar Talata.

Ya bayyana cewa ya kamata a wayar da kan mutane game da gyaran tituna da ake yi a jihar.

Waɗanda abin ya shafa galibin mata ne da yara ƙanana da ke tsallaka titi.

KU KUMA KARANTA: Mutum 16 sun mutu, 27 sun jikkata a hatsarin tirela a Kaduna

Danladi ya gargaɗi direbobi da su yi taka-tsan-tsan tare da rage gudu don guje wa yanayin da ba a shirya masa ba.

A cewarsa, duk da cewa ma’aikatan hukumar suna kan hanyoyin don saukaka zirga-zirga, amma akwai bukatar kamfanonin gine-ginen da ke gudanar da ayyukan tituna a jihar su samar da isassun alamun hanyoyin don jan hankalin masu ababen hawa da jama’a.

Ya yi ƙira ga gwamnati da ta faɗakar da jama’a kan yadda za a yi amfani da hanyoyi a wannan lokaci na ayyukan gyaran tituna, la’akari da sauye-sauyen tsarin zirga-zirga.

Danladi ya ce ya kamata gwamnati ta ɗauki nauyin wayar da kan jama’a a kafafen yaɗa labarai game da hanyoyin da ake gyara don kauce wa rasa rayuka da dukiyoyi.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *