No menu items!

Sample Page Title

Date:

Kimanin mutum 40 ne ake zullumin sun ɓace bayan wani hatsarin kwale-kwale a yankin ƙaramar hukumar Yauri a Jihar Kebbi.

Aminiya ta gano cewa kwale-kwalen ya yi hatsari ne yayin da yake ɗauke da kaya da fasinjoji kimanin 50 a kan Kogin Neja a rnaar Litinin.

Shugaban ƙaramar hukuumar Yauri, Alhaji Bala Mohammed, ya ce fasinjojin da kwale-kwalen sun taso ne daga ƙauyen Kasabo a ƙaramar Hukumar Agura na Jihar Neja a hanyarsu ta zuwa Yauri inda suka yi hatsari.

Ya ce hatsarin kwale-kwale ya auku ne sakamakon ƙarfin igiyar ruwa, kuma mutum 10 ne aka yi nasarar ceto wa zuwa lokacin da muka samu wannan rahoto.

Amma ya ce “ana ci gaba da aikin ceto” da fatan sauran ma za a same su da ransu.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...