No menu items!

Sample Page Title

Date:

Aƙalla mutum huɗu ne suka mutum a lokacin da babbar motar dakon kaya ta yi awon gaba da wata bus da Keke Napep.

Al’amarin ya faru ne a ranar Talata a kan gadar Ogbor-Hill da ke garin Aba a jihar Abiya, lokacin da burkin babbar motar dakon kayan ya shanye.

Rahotanni sun ce bayan faruwar haɗarin, mutane sun rika fito da fasinjojin ababen hawan da babbar motar ta take, sai dai baya ga waɗanda suka rasu, akwai ƙarin mutane da dama da suka samu munanan raunuka.

Wani ganau ya ce ‘mun rika ciro mutanen ne saboda babu motar janwe da za a yi anfani da ita wajen fito da ababen hawan da ke karkashin babbar motar.’

An hango Jami’an Hukumar Kiyaye Haddura ta Kasa FRSC a wajen da abun ya faru.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...