Mutum 32 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Taraba

Aƙalla mutum 32 da suka haɗa da yara 20 da manya 12 ne suka rasa rayukansu a wani hatsarin kwale-kwale a garin Ibbi da ke ƙaramar hukumar Ibbi a jihar Taraba.

Kwale-kwalen na ɗauke da masunta sama da 50 daga garin Ibbi zuwa Gabashin jihar a ranar asabar don yin su a yayin da ya kife a kusa da gaɓar kogin Benuwai.

Wani mazaunin garin Ibbi, Malam Ibrahim Ibbi, ya ce yara 20 da manya 12 ne suka mutu a hatsarin.

Gwamnan jihar, Agbu Kefas, ya bayyana lamarin a matsayin abun taƙaici, kwanaki kaɗan bayan faruwar wani hatsarin jirgin ruwan a Karim Lamido.

Ya jajanta wa al’ummar Ibbi tare da addu’ar Allah Ya jikan waɗanda suka rasu.

KU KUMA KARANTA: Manoma 4 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Nasarawa

Gwamna Kefas, ya ce gwamnati ta tashi tsaye wajen gudanar da bincike domin gano musabbabin yawan hatsarin kwale-kwale a jihar.

Gwamnan ya ce nan ba da jimawa da kansa zai zagaya yankunan da abin ya shafa da nufin ganawa da masu ruwa da tsaki a harkar sufurin ruwa.

Kazalika ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da aiki don ƙare rayukan al’ummar jihar.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *