Mutum 2 sun mutu a wani fashewar bom
Mutane biyu ne suka mutu sakamakon fashewar wani abu a wani rukunin gidaje dari biyu da ake ginawa a garin Dalwa na jihar Borno.
Bayanan da ake samu sun nuna cewa fashewar ta faru ne da misalin karfe 1 na ranar Laraba a daidai lokacin da gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum; da takwaransa na Yobe, Mai Mala Buni, sun ƙaddamar da gidaje a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Wata majiya ta shaida wa News Point Nigeria cewa irin wannan lamari ya afku a ranar Talata amma babu cikakken bayani kan fashewar ta ranar Talata.
KU KUMA KARANTA: Bom ya kashe kwamandojin JTF da dakarunsu a Borno
Dalwa dai yana da tazarar kilomita 175 daga Maiduguri kuma yana ɗaya daga cikin al’ummomin da ‘yan Boko Haram suka lalata tare da raba su da muhallansu.
Zulum ya fara aikin sake gina al’ummar Dalwa da gidaje dari biyu