No menu items!

Sample Page Title

Date:

Mutane 16 sun rasu, wasu 30 sun samu rauna a hatsarin babbar mota a yankin Jos da ke jihar Filato.

Wata tirela makare da kaya da mutane ce ta yi dungure ta faɗa a wani rami, inda mutum 11 suka rasu nan take, wasu kimanin 30 suna samu raunuka.

Kwamndan Hukumar Kiae Haɗɗura a Ƙasa (FRSC) a jihar Filato, Alphonsus Halim Godwinya ce, “karin wasu 5 sun rasu daga bisani a asibiti.”

Jami’in ya bayyana cewa motar ta fito ne daga Jihar Kano za ta Abuja, lokacin da ta samu hatsarin a Hauwan-Kibo da ke ƙaramar hukumar ta Jos Kudu.

KU KUMA KARANTA: Mutum 6 sun mutu sakamakon hatsarin mota a Zamfara 

Alphonsusya ce wasu daga cikin waɗanda suka samu raunin an kai su asibitin sojoji, waɗanda suka samu rauni mai tsanani kuma an kai su Asibitin Koyarwa na Jami’ar Jos (JUH).

Ya ce hatsarin ya auku ne sakamakon tsinkewar burkin motar wadda ke ɗauke buhunan hatsi. 

Da haka ta roki matafiya da su guji neman saukin kuɗin mota sa ya sa aloda su a cikin motocin ɗaukar kaya.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...