Mutum 16 sun mutu, 27 sun jikkata a hatsarin tirela a Kaduna

Hatsarin tirela ya yi ajalin mutane 16 yayin da wasu 27 suka samu raunuka a jihar Kaduna.

Kwamandan Hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa (FRSC) a jihar, Kabir Nadabo ya ce hatsarin ya auku ne ranar Lahadi.

Nadabo ya ce wata tirela kirar DAF dauke da mutane 65 ce ta kwace ta fada a cikin wani rami da asuba.

Ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne a kusa da ƙauyen Audu Jangwam a kan Babbar Hanyar Kaduna-Abuja.

Yana yi zargin hatsarin ya auku ne a sakamakon gudun wuce ƙa’ida da kuma gajiyar direba.

KU KUMA KARANTA: Hatsarin tirela ya yi ajalin mutum 11 a Kebbi

Ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) cewa an kai waɗanda suka jikkata asibiti

Jami’an hukumar na aikin ceto domin kawar da motar, wadda ta ɓarinta ya tare hanyar.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *