Mutanen da yunwa ta kashe a Gaza sun kai 18 — Ma’aikatar Lafiya

Ma’aikatar Lafiya ta Falasɗinu ta ce adadin Falasɗinawan da suka mutu sakamakon yunwa a Gaza ya ƙaru zuwa 18 sakamakon takunkuman da Isra’ila ta ƙaƙaba musu.

A cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar Ashraf al Qudra ya fitar, ya ce “yunwa a arewacin Gaza ta kai matakin illata mutane, musamman ga yara da mata masu juna biyu da masu fama da cututtuka masu tsanani.

Ya yi gargaɗin cewa dubban mutane na cikin haɗarin mutuwa saboda yunwa, inda ya yi ƙira da a gaggauta kai agajin jinƙai da jinya ga yankin Falasɗinu.

KU KUMA KARANTA: Matakan da gwamnatin Najeriya ta ɗauka na ƙayyade farashi ba zai kawar da yunwa ba – Masana

Kakakin ya zargi sojojin Isra’ila da “da aikata mummunan kisan kiyashi da gangan akan dubban mutanen da ke fama da yunwa a arewacin Gaza.”

Ya yi ƙira ga Majalisar Ɗinkin Duniya da ta dauki matakan gaggawa “don hana afkuwar bala’in jinƙai da lafiya a arewacin Gaza.”


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *