Mutanen da Isra’ila ta kashe a Gaza sun ƙaru – Rahoto
Adadin mutanen da suka rasa rayukansu a hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai a Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoban 2023, ya ƙaru da 28 a cikin sa’o’i 24 da suka wuce, inda yawan ya kai 44,786.
A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Lafiya ta Falasɗinu a Gaza ta fitar, an bayar da bayanai dangane da hare-haren da Isra’ila ke kai wa Gaza tsawon kwanaki 431.
An bayar da rahoton cewa, mutume 28 ne suka rasa rayukansu kana wasu 54 kuma suka samu raunuka sakamakon kisan kiyashi huɗu da sojojin Isra’ila suka yi a sassa daban-daban na Gaza cikin sa’o’i 24 da suka gabata.
KU KUMA KARANTA: Masu zanga-zanga a Isra’ila sun zargi Netanyahu da ƙin kawo ƙarshen yaƙin da ƙasar ke yi a Gaza
An yi kiyasin cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoban 2023, ya ƙaru zuwa 44,786 sannan adadin waɗanda suka jikkata ya ƙaru zuwa 106,188