Mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri ‘na fuskantar matsalar lafiya’ – NRC
Wata hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Najeriya,ta bayyana cewa, ana fama da matsalar jinƙai a jihar Borno, bayan da mummunar ambaliyar ruwa ta raba mutane sama da miliyan guda da muhallansu tare da gajiyar da ma’aikatan lafiya.
Yankin da tuni yake fama da matsalar ta da ƙayar bayan da aka daɗe ana fama da shi, yanzu haka yana fuskantar yiwuwar ɓullar cututtuka masu yaɗuwa ta ruwa.
Ambaliyar ruwan wadda ita ce mafi muni cikin shekaru 30 da suka gabata, ta yi sanadin mutuwar mutum fiye da 30.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta ƙasar Norway NRC ta bayyana cewa, a ƙarshen mako, an samu ƙarin mutum 50,000 da suka rasa matsugunansu a arewa maso gabashin Najeriyar, yayin da ambaliyar ruwa ta tsananta.
“Halin da ake ciki a yankin Sahel da Tafkin Chadi yana ƙara ta’azzara, saboda illar tashe-tashen hankula, da matsugunai, da sauyin yanayi na yin illa ga masu rauni,” in ji Hassane Hamadou, daraktan yankin tsakiya da yammacin Afirka ta NRC.
Yawancin mutanen da suka rasa matsugunansu suna zaune ne a sansanoni ba tare da samun abinci ko tsaftataccen ruwan sha ba, lamarin da ya sa suke fama da rashin lafiya musamman.
KU KUMA KARANTA: Ba mu gama tantance adadin waɗanda suka rasa rayukansu a ambaliyar ruwa a Maiduguri ba – NEMA
Lamarin dai ya ƙara ta’azzara ne sakamakon matsin da hukumomin agaji da albarkatun gwamnati ke fuskanta.
Ambaliyar ruwa a Borno, cibiyar Boko Haram, ya samo asali ne sakamakon wani dam da ya ɓalle bayan ruwan sama kamar da bakin ƙwarya.
Irin wannan ambaliya ta afku a wasu sassan yankin Sahel da suka haɗa da Kamaru, Chadi, Mali, da Nijar.
A cikin makonni biyu da suka gabata, ambaliyar ruwa a yammacin Afirka da tsakiyar Afirka ta yi sanadiyar raba mutane sama da miliyan 1.5 da muhallansu tare da haddasa mutuwar kusan 465 a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.
A arewa maso gabashin Najeriya kaɗai, an samu ƙarin mutane 50,000 da suka rasa matsugunansu a ‘yan kwanakin nan.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Norway NRC, ta yi gargaɗi game da mummunan halin da ake ciki a yankin, inda ta bayyana illolin da tashe-tashen hankula, da raba mutane da matsugunansu, da sauyin yanayi ke haifarwa ga jama’a masu rauni.
A Maiduguri, babban birnin jihar Borno, daruruwan mutane na dakon ganin likitoci, saboda da dama daga cikinsu na fama da cututtuka kamar gudawa. Bintu Amadu, wacce ɗanta ba shi da lafiya, ta bayyana takaicinta na neman magani ba tare da samun nasara ba.
Ramatu Yajubu, duk da cewa an ba ta lokacin ganin likita, ta shiga rashin tabbas game da ganin nasa, saboda yadda mutane suka yi yawa.
Mathias Goemaere na ƙungiyar likitoci ta Médecins Sans Frontières (MSF) ya jaddada karuwar hadarin kamuwa da cututtuka na ruwa a tsakanin al’ummar da ke fama da rashin abinci mai gina jiki da rarraunan tsarin rigakafi.
Gwamnatin Najeriya ta fitar da wani gargaɗi game da ƙaruwar ruwa a kogin Benuwai da Neja, lamarin da ka iya janyo ambaliya a yankin kudancin Neja Delta.