Mutane sun fasa rumbun ajiyar kayayyaki na Majilisar Ɗinkin Duniya

0
261

Tun da safe, an ta kai hare-hare, mita 50 daga asibitin,” a wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a shafin X.

Majalisar Ɗinkin Duniya tace a ranar lahadin nan dubban mutane sun fasa ɗakunan ajiyar kayayyakin agaji na Majalisar da ke Gaza.

Majalisar ta ce mutanen sun kwashi fulawa da sauran kayayyakin buƙatun yau da kullum.

Thomas White wanda darakta ne a hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya ce fasa ɗakunan ajiyar wata alama ce da ke nuna doka da oda ta soma yankewa sakamakon matsi da jama’a ke ciki.

Ƙungiyar agaji ta Palestinian Red Crescent ta bayyana hukumomin Isra’ila sun mata babbar barazana kan cewa su tattara su bar asibitin Al Quds da ke Gaza sakamakon suna da niyyar kai masa hari.

KU KUMA KARANTA: Ta nemi Majalisar Ɗinkin Duniya ta ƙaddamar da yaƙi kan yin hijira ba bisa ƙa’ida ba

“Tun da safe, an ta kai hare-hare mita 50 daga asibitin,” a wata sanarwa da kungiyar ta fitar a shafin X.

Isra’ila ta kai hari kusa da asibiti mafi girma da ke Gaza, kamar yadda mazauna suka tabbatar.

Mazaunan sun ce harin da Isra’ila ta kai ya lalata hanyoyin da za su kai ga asibitin, wanda asibitin ya kasance wata mafaka ga ɗimbim Falasɗinawa da ke guje wa hare-haren Isra’ila.

Wannan na zuwa ne yayin da Isra’ilar ke ci gaba da zafafa hare-hare a Gaza.

Leave a Reply