Mutane shida a Kaduna sun mutu sakamakon harin ‘yan bindiga

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane shida a wani sabon hari da suka kai a ƙauyen Takanai da ke ƙaramar hukumar Zango Kataf a jihar Kaduna.

Rahotanni sun ce harin ya faru ne da misalin ƙarfe 7 na dare, ranar Talata. Wani mazaunin unguwar Samson Markus, wanda ya tabbatar wa manema labarai harin a ranar Laraba, ya ce lamarin ya faru “lokacin da ba a yi tsammani ba”.

A cewarsa, waɗanda abin ya shafa sun haɗa da ƙananan yara biyu da kuma ‘yan gida ɗaya.

“ ‘Yan bindigan sun zo ne da misalin ƙarfe 7 na dare lokacin da ba mu yi tsammanin irin wannan abu na iya faruwa ba.

KU KUMA KARANTA: Harin makami mai linzami a Yukren ya kashe mutane 16

Muna cikin harkokinmu na yau da kullum, kwatsam sai muka ji ƙarar harbe-harbe.

“Kowa ya fara gudu don tsira. An kashe mutane huɗu daga iyali ɗaya da kuma wasu biyu daga gida ɗaya, ciki har da yara biyu,” in ji Mista Markus.

A cewarsa, ‘yan bindigar sun tsere daga yankin kafin isowar jami’an tsaro. Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ba ta ce uffan ba kan lamarin har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *