Mutane biyu sun rasa rayukansu sakamakon ɗauko wayar salula a masai a Jihar Kano

0
286
Mutane biyu sun rasa rayukansu sakamakon ɗauko wayar salula a masai a Jihar Kano

Mutane biyu sun rasa rayukansu sakamakon ɗauko wayar salula a masai a Jihar Kano

Daga Shafaatu Dauda Kano

Hukumar Kashe Gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar mutane biyu a yayin kokarin dauko waya da ta fada a shadda a yankin karamar hukumar Albasu dake jihar.

Wata sanarwa da Jami’in Hulda da Jama’a na hukumar, ACFO Saminu Yusuf Abdullahi ya fitar a ranar Lahadi ta ce a ranar Asabar 21 ga watan Yunin 2025, ofishin hukumar dake karamar hukumar Takai ya samu kiran neman dauki daga sufeto Auwalu, inda ya ba da rahoton fadawar mutanen biyu shadda a unguwar Bazabe ta karamar hukumar Albasu.

Ya ce a sakamakon haka ne suka tura jami’ansu na karamar hukumar Takai wadanda suka isa wurin da misalin karfe 11:16.
Ko da suka isa, sai suka tarar wani mutum mai suna Usman Muhammad dan kimanin shekaru 40, wanda ya shiga ramin shaddar da nufin dauko wayarsa da ake kira ‘Indon Ƙauye’ da ta fada ramin, ya kasa fitowa daga ciki.

KU KUMA KARANTA: Injin niƙa ya gutsire kan wata mata a Kaduna

Mutum na biyu mai suna Ibrahim Inuwa shi ma dan kimanin shekaru 40 a duniya, ya shiga ramin shaddar da nufin taimakawa wajen fito da mutum na farko.

Kakakin hukumar kashe gobarar ta jihar Kano ya ce mutumin ya samu nasarar daura igiyar da ake kokarin fito da su da ita amma sai ya fita daga hayyacinsa wanda hakan ta sa ya gaza fitowa daga ramin.

Saminu Yusuf Abdullahi ya ce sun sami nasarar fito da mutanen biyu daga ramin shaddar amma ba sa cikin hayyacinsu, inda daga bisani aka tabbatar da rasuwarsu baki daya.

Tuni dai aka mika gawarwakin mutanen biyu ga Babban Baturen ‘Yan Sanda na karamar hukumar Albasu, Kabiru Magawata.

Leave a Reply