Mutane biyu sun mutu, takwas sun jikkata sakamakon fashewar bam a jihar Borno

0
128

Daga Sani Gazas Chinade, Maiduguri 

Wani fashewar Bam ya kashe a ƙalla jami’an tsaron farin kaya na Civilian Joint Task Force (CJTF) guda biyu ne a ƙaramar hukumar Mafa da ke jihar Borno, yayin da wasu takwas suka samu raunuka dabam-dabam sakamakon fashewar wani abu da ya faru da su.

Majiyar tsaro da ke garin na Mafa na nuna cewar wannan lamarin ya faru ne a ranar Talata a lokacin da jami’an tsaron na CJTFsuke gudanar da ayyukansu na sintiri a yankin ƙaramar hukumar Mafa da Konduga yadda suka taka wata nakiya da ake zargin mayaƙan Boko Haram ne suka binne.

A rahoton da aka tattare na bayyana cewa mutanen biyu daga cikin ‘yan CJTF  sun mutu ne nan take a wajen da Bam ɗin ya tashi yayin da sauran mambobin takwas suka samu raunuka dabam-dabam yadda aka garzaya da su asibitin koyarwa na jami’ar Maiduguri.

KU KUMA KARANTA: Mutane biyu sun mutu, 77 sun jikkata a fashewar da ta faru a Ibadan

An yi jana’izar su a garin Mafa da yammacin ranar Talata kamar yadda addinin Musulunci ya tanada tare da yi musu addu’ar Allah ya gafarta wa mamatan ya kuma  baiwa iyalansu ƙarfin gwuiwa dangane da hasarar suka yi da da ba za a iya mantawa da su ba.

Shugaban ƙaramar hukumar Mafa Hon. Goni Gonibe, tare da ɗan majalisar dokokin jihar Borno (BOSHA) mai wakiltar Mafa mai wakiltar mazaɓar a majalisar dokokin jihar, Hon Baba Ali Modu, sakataren ƙaramar hukumar Mafa, Alhaji Sale Bukar, da kwamandan rundunar ta CJTF a  Mafa da sauran al’umma sun halarci jana’izar.

Leave a Reply