Mutane 7 sun ɓace bayan hatsarin jiragen helikwaftan sojin Japan

Jami’ai sun ce mutane bakwai ne suka ɓace tun bayan da wani hatsari ya faru cikin dare, wanda ya rutsa da jirage biyu samfurin helikwafta na sojin Japan a tsakiyar teku.

Wani kakakin Hukumar Tsaron-Kai ta Japan (SDF), ya tabbatar wa da kamfanin dillancin labarai na AFP a maraicen Asabar, cewa hatsarin ya faru, inda ya ce an ceto mutum guda.

Ministan Tsaro na Japan, Kihara Minoru ya ce masu ceto “sun gano abubuwan da suka yi kama da ɓangaren jirgin saman a cikin teku, kuma sun yi imani jiragen biyu sun yi hatsari.”

Kihara ya faɗa wa maneman labarai cewa, “A daidai yanzu, ba a san musabbabin hatsarin ba, amma muna iya ƙoƙarinmu don ceto rayuka”.

Alamu sun nuna cewa jiragen helikwaftan sun yi hatsari ne yayin wani atisaye na cikin dare, gab da tsibirin Izu da ke tekun Pacific, a cewar rahotannin gidan jaridar NHK.

KU KUMA KARANTA: Babban Hafsan Sojojin Kenya, Francis Ogollaya, ya mutu a hatsarin helikwafta

Rahotan NHK ya nuna cewa sadarwa da ɗaya cikin jiragen ta katse ne da ƙarfe 10:38 na yamma (13:38 GMT) kusa da tsibirin Torishima, sannan minti ɗaya bayan nan an samu sanarwar gaggawa daga wannan jirgin.

Bayan kamar minti 25, da wajen ƙarfe 11:04 na yamma, sojojin sun gano cewa sadarwa da ɗayan jirgin ta katse shi ma a dai wuri ɗaya.

Jiragen helikwafta ƙirar Mitsubishi SH-60K daga Rundunar Ruwa ta Tsaron-Kai (MSDF) sun fi yin aiki ne kan jiragen ruwan yaƙi.

NHK ta ƙara da cewa, hukumar MSDF ta ce babu wani jirgin sama ko na ruwa a kusa da wajen, kuma ba a tunanin akwai hannun wata ƙasa a hatsarin.

Japan tana ƙara kashe kuɗaɗe wajen harkokin tsaro, kuma tana zurfafa haɗin gwiwa tare da Amurka da sauran ƙasashe a nahiyar Asiya, don martani kan ƙaruwar nuna ƙarfi da China ke yi a yankin, da kuma barazanar da Koriya ta Arewa ke nunawa.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *