Mutane 56 da aka kama aka yi garkuwa dasu a garin Kafin Koro, an ba da wa’adin biyan kuɗin fansa

0
650

Wasu mutane 56 da aka yi garkuwa da su a ƙauyen Kaffin-Koro da ke ƙaramar hukumar Paikoro a jihar Neja sun yi kukan neman agaji a wani faifan bidiyo da ɓarayin suka fitar.

Jaridar DAILY NIGERIAN  ta rawaito cewa a ranar 10 ga watan Mayu, ‘yan ta’addan sun aukawa garin Kaffin-Koro inda suka yi garkuwa da mazauna garin 56, waɗanda galibinsu manoma ne da ‘yan kasuwa.

DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa wasu daga cikin waɗanda abin ya shafa an sako su bayan iyalansu sun biya kuɗin fansa ga ‘yan ta’addan.

Wata majiya da aka sako ‘yan uwanta kwanan nan daga sace su ta tabbatar da biyan kuɗin fansa da dangin suka yi.

“Mun biya Naira miliyan 7.5 kafin a sako ‘yan uwanmu a ranar Litinin”, majiyar da ta nemi a sakaya sunanta ta ce.

A cikin faifan bidiyon da DAILY NIGERIAN ta samu, an ga ‘yan bindigar suna zaluntar waɗanda aka kama tare da yin barazanar kashe su.

Wasu daga cikin waɗanda suka yi garkuwa da su, an ɗaure su ne da sarƙa a ƙafa, yayin da matan da aka yi garkuwa da su aka bar su a tsaye, kuma ‘yan ta’adda masu riƙe da bindigogi sun kewaye su.

KU KUMA KARANTA: ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da mata biyu, shugabannin jam’iyyar APC a Kaduna

‘Yan ta’addan da suka fito da yawa a cikin faifan bidiyon duk suna ɗauke da bindigogi ƙirar AK-47.

A ɗaya daga cikin faifan bidiyon, wani ɗan fashi ya harbi ƙafafun wanda aka kama domin nuna muhimmancin biyan kuɗin fansa.

Haka kuma an ga wani ɗan ta’addan yana nuna wata mata da ke neman a taimaka masa da bindiga ya harbeta, amma bai yi nasara ba.

An kuma ga wani dattijo, mai ɗauke da rauni a ɗaɗɗaure da sarƙa a ƙafa yana jan ƙafa a ɗaya daga cikin bidiyon.

An ce ‘yan fashin sun ba da wa’adin ga iyalan waɗanda abin ya shafa su biya kuɗin fansa ko kuma su rasa ‘yan uwansu.

Wani mazaunin garin Kaffin Koro da ya zanta da wakilinmu da ya nemi a sakaya sunansa ya ce tun lokacin da aka fitar da bidiyon al’ummar yankin sun jefa al’ummar yankin cikin firgici.

“Bidiyon ya yaɗu kuma ya kasance abin tattaunawa a cikin al’umma, amma ban iya kallon shi ba saboda ‘yar’uwata ta kasance a cikin waɗanda aka kashe.

Mutane da yawa sun iya gano ‘yan uwansu a cikin wannan mugunyar bidiyo,” in ji shi.

Da aka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Biodun Wasiu, ya ce ‘yan sandan na aiki tare da haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da jihohi maƙwabta domin ceto waɗanda lamarin ya rutsa da su.

“Muna aiki da sauran hukumomin tsaro, musamman sojoji, kuma muna haɗin gwiwa da sauran jihohin da ke maƙwabtaka da su don ganin an kuɓutar da su daga hannun waɗanda ake garkuwa da su,” in ji Mista Abiodun.

Babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan jihar, Bologi Ibrahim, bai mayar da martani ga saƙon SMS da aka aike zuwa layinsa ba a lokacin da aka gabatar da wannan rahoto.

Leave a Reply