Mutane 32 sun mutu a hatsarin kwale-kwale a Borgu ta jihar Neja
An kawo ƙarshe aikin ceton da aka gudanar domin ceto mutanen da suka nutse sakamakon hatsarin kwale-kwale da ya faru a yankin Borgu da ke jihar Neja a Najeriya.
Lamarin da ya faru a ranar Talata ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 32.
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar, Abdullahi Baba Ara, ya bayyana wa BBC cewa kusan duk waɗanda ake tunanin suna cikin kwale-kwalen da ya yi hatsari an gama aikin ceto a wurin.
Ya ce, “Har an yi jana’izar waɗanda suka mutu, kuma waɗanda suka jikkata an garzaya da su asibiti inda aka ba su kulawa, kuma yawanci dukansu an sallamesu.”
Baba Ara ya ƙara da cewa, “Bayani na ƙarshe da aka tantance zuwa jiya da dare ya nuna cewa mutum aƙalla 32 ne suka rasa rayukansu, yayin da guda 50 aka ceto. Muna kyautata zaton cewa saura mutum takwas da ba a gansu ba, amma ba za muyi ƙasa a gwiwa ba wajen aikin ceto su.”
KU KUMA KARANTA: Mutane 35 sun ɓace a cikin ruwa, sakamakon kifewar kwale-kwale a Zamfara
Ya bayyana cewa hatsarin ya faru ne saboda kwale-kwalen ya yi lodin wuce kima, wato ɗaukar kaya da mutane fiye da yadda ya kamata.
Hakanan, yayin da jirgin ke tafiya cikin ruwa, ya bugi kututture na icce, wanda ya haifar da kifewar kwale-kwalen.
Dangane da dokokin da ke tabbatar da cewa jiragen ruwa ba sa yin lodin wuce kima, Baba Ara ya ce, “Akwai doka, amma kasan al’amari na ɗan adam, yawanci wasu ba sa bin waɗannan dokokin.”
Hukumar ta ce za ta ci gaba da wayar da kan jama’a kan muhimmancin bin ka’idojin tsaron ruwa domin rage aukuwar irin wannan hatsari a nan gaba.









