No menu items!

Sample Page Title

Date:

Mutane 3 sun mutu a wani rikicin coci

Rundunar ’yansandan Jihar Taraba, ta tabbatar da mutuwar mutum uku sakamakon rikici da ya faru tsakanin mabiya cocin United Methodist Church in Nigeria (UMCN) da kuma na Global Methodist Church (GMC).

Kakakin rundunar ’yan sandan, SP Usman Abdullahi, ya bayyana cewa rikicin ya faru ne a ranar Lahadi a Ƙaramar Hukumar Karim-Lamido.

Rahotanni, sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne sakamakon wata taƙaddama tsakanin mambobin cocin biyu.

Rikicin ya sa gwamnatin jihar bayar da umarnin rufe hedikwatar cocin UMCN da ke Jalingo.

KU KUMA KARANTA: Mutane fiye da 100 sun mutu sakamakon rikicin da ya ɓarke a filin ƙwallon ƙafa

Rundunar ta ce an kama mutum shida da ake zargi da hannu a rikicin, sannan an tura jami’an tsaro yankin domin tabbatar da zaman lafiya.

Bincike, ya nuna cewa taƙaddamar ta samo asali ne daga rikicin shugabanci tsakanin UMCN da GMC, wanda ya raba kan mambobin cocin gida biyu, har wasu suka ware tare da kafa nasu tsagin.

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...