Mutane 27 sun mutu a rikicin da ya ɓarke a ƙasar Libya

Kimanin mutane 27 ne suka mutu yayin da 106 suka samu raunuka sakamakon arangamar da aka yi tsakanin ɓangarorin da ke gaba da juna a babban birnin ƙasar Libya mai fama da rikici, a cewar wata hukumar lafiya ta ƙasar.

Cibiyar bayar da agajin gaggawa ta Libya ta ce an kwashe wasu iyalai 230 daga yankin da rikicin ya ɓarke, musamman a yankunan gabashi da kudu maso gabashin birnin Tripoli.

Hukumar ba ta bayyana adadin farar hula nawa ba a cikin waɗanda aka kashe.

Rikicin ya ɓarke ne a daren jiya litinin tsakanin runduna ta 444 dake samun goyon bayan ma’aikatar harkokin cikin gida a birnin Tripoli da kuma ‘yan adawar Deterrence Force bayan da sojojin suka kama babban kwamandan Brigade ta 444 Mahmoud Hamzah.

A cewar majiyoyi a babban birnin ƙasar Libya, kwanciyar hankali ta kwanta a ranar Laraba bayan da aka ce an miƙa Hamza ga wani ɓangare na tsaka mai wuya.

KU KUMA KARANTA: Mutane 30 sun mutu a Rasha, sakamakon tashin gobara a gidan mai

An dakatar da zirga-zirgar jiragen sama zuwa filin jirgin saman Mitiga da ke kusa a ranar Talata a cikin tashin hankalin, kuma an dakatar da azuzuwa a Jami’ar Tripoli.

Za su sake komawa ranar Asabar, in ji jami’ar. Ƙasar Libya dai ta faɗa cikin ruɗani tun bayan hamɓarar da gwamnatin marigayi Moamer Gaddafi a shekara ta 2011.

A halin yanzu dai gwamnatoci biyu ne ke neman mulki.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *