Fasinjoji 18 ne suka mutu a wani hatsarin mota da ya auku a ranar Juma’a a garin Zakirai dake kan titin Kano zuwa Ringim a ƙaramar hukumar Gabasawa ta jihar Kano.
Hakazalika wasu mutane 12 sun samu raunuka a hatsarin yayin da biyar suka tsira ba tare da wani rauni ba, kamar yadda kwamandan hukumar FRSC reshen jihar, Ibrahim Abdullahi ya bayyana.
An yi jana’izar wasu gawarwakin a wurin da hatsarin ya auku, yayin da wasu kuma aka miƙa su ga ‘yan uwansu.
Abdullahi ya tabbatar a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun sashen, Abdullahi Labaran ya fitar cewa hatsarin ya rutsa da motocin kasuwanci guda biyu.
KU KUMA KARANTA: Hatsarin mota ya ci rayukan mutane 14, ya jikkata 5 a Bauchi
“Mun samu waya game da haɗarin da misalin ƙarfe 8:35 na dare, a ranar Juma’a kuma muka tura jami’an mu wurin domin ceto waɗanda abin ya shafa,” in ji Abdullahi.
Ya ɗaura laifin hatsarin da gudun wuce gona da iri, da tuƙin ganganci da kuma lodin wuce ƙa’ida, sannan motar ta kama da wuta tare da ƙona ɗaya daga cikin motocin.
“Hatsarin ya haɗa da fasinjoji 35 a cikin motocin bas guda biyu, daga cikinsu 18 sun ƙone ƙurmus, yayin da wasu 12 suka samu munanan raunuka,” in ji shi.
Ibrahim ya ce an kai waɗanda suka jikkata zuwa babban asibitin Murtala Mohammed da ke Kano.
Ya shawarci masu ababen hawa da su guji gudun wuce gona da iri, yin lodi fiye da kima, tuƙin ganganci da kuma duk wani saɓani da ka iya haifar da haɗarurruka.
Kwamandan sashin ya bayyana nadamarsa game da girman haɗurran hanyoyin da za a kaucewa gujewa a jihar Kano a makon da ya gabata.
A ziyarar da ya kai wurin da hatsarin ya auku a ranar Asabar, ya gargaɗi masu ababen hawa, musamman masu zirga-zirgar ababen hawa da na jahohi da su daina yin lodi fiye da ƙima, da gudun wuce gona da iri da dai sauransu.
Abdullahi ya ba da tabbacin hukumar FRSC za ta ƙara wayar da kan jama’a tare da ɗaukar tsauraran matakan tsaro, gami da gudanar da ayyukan kotunan tafi-da-gidanka don daƙile yawaitar haɗurran motoci a tsakanin gari.
[…] KU KUMA KARANTA: Mutane 18 sun mutu, 12 sun samu raunuka, sakamakon hatsarin mota a Kano […]
[…] KU KUMA KARANTA: Mutane 18 sun mutu, 12 sun samu raunuka, sakamakon hatsarin mota a Kano […]
[…] KU KUMA KARANTA: Mutane 18 sun mutu, 12 sun samu raunuka, sakamakon hatsarin mota a Kano […]