Mutane 18 sun jikkata bayan da wata motar APC ta auka cikin taron mutane a Jigawa
Daga Shafaatu Dauda Kano
Akalla mutane 18 ne suka jikkata a ranar Lahadi 10 ga Agusta, bayan wata motar haya dauke da magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta afka cikin wani taro a Karamar Hukumar Ringim ta Jihar Jigawa.
Wadanda abin ya rutsa da su sun taru ne a gefen hanya a kauyen Yakasawa, kimanin kilomita biyu daga garin Ringim, domin tarbar Gwamna Umar Namadi a bikin baje kolin shirin “Hadin gwiwa tsakanin ‘yan kasa da gwamnati” karo na 15, wanda gwamnatin jihar ta shirya domin kusantar da gwamnati ga jama’a.
Ganau sun shaida wa Manema labarai cewa wata motar Golf Volkswagen mai lambar rijista FKJ 102 JB ta kauce wa hanya, sannan ta afka cikin taron jama’a.

Wani shaida, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce direban bai rike motar yadda ya kamata ba, sannan cikin lokaci kadan ta karkata ta nufi inda mutane suke tsaye a gefen hanya.
“A lokacin bamu damu da gane wadanda abin ya rutsa da su ba, burinmu kawai shi ne a garzaya da su asibiti domin samun kulawar gaggawa,” in ji shi.
Bayan hadarin, mazauna yankin sun taimaka wajen ceto wadanda abin ya rutsa da su, suna fitar da su daga cikin motar zuwa wuri mai aminci kafin motar hukumar kiyaye hadurra ta FRSC ta iso don kai su asibiti.
KU KUMA KARANTA: A wata 6, hatsarin mota ya kashe sama da mutane 2,800 – FRSC
Wani ganau mai suna Saminu Shehu ya ce, “An garzaya da su Asibitin Gwamnatin Ringim cikin motar FRSC domin samun kulawa.”
Mai magana da yawun Hukumar Tsaro ta NSCDC a Jigawa, ASC Badruddeen Tijjani, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa binciken farko ya nuna direban yana gudu sosai sannan ya yi yunkurin kauce wa rami kafin hadarin ya auku.
“Motar na dauke da fasinjoji lokacin da ta fita daga hanya ta afka cikin taron mutane, wanda hakan ya shafi jimillar mutum 18,” in ji shi.
Ya ce babu wanda ya mutu, amma duk wadanda abin ya shafa sun samu raunuka iri daban-daban.
“An garzaya da su Asibitin Gwamnatin Ringim domin samun magani ta hannun jami’an NSCDC da FRSC,” ya kara da cewa.
Tijjani ya ce hukumar za ta gudanar da bincike na musamman domin gano musabbabin lamarin da kuma kauce wa faruwar irin haka nan gaba, tare da jan hankalin direbobi su yi taka-tsantsan musamman a wuraren da ke da ramuka.
Ya kuma yaba da gaggawar amsa kiran gaggawa da jami’an NSCDC da FRSC suka yi wanda ya ba da damar ceto wadanda suka jikkata cikin lokaci.









