Mutane 15 sun mutu, 36 sun jikkata a hatsarin motar bas mai ɗauke da baƙin haure

Wata motar bas da ke jigilar galibin baƙin haure ‘yan ƙasar Venezuela ta yi hatsari a tsakiyar ƙasar Mexico a ranar Talata, inda aƙalla mutane 15 suka mutu sannan wasu 36 suka jikkata, kamar yadda hukumomi suka bayyana.

Motar ta yi karo da wata tirela a kan babbar hanyar da ta haɗa jihohin Puebla da Oaxaca, gwamnatin Puebla ta bayyana a dandalin sada zumunta na X, wanda a da ake ƙira Twitter.

“Abin takaici mutane 15 ne suka rasa rayukansu sannan wasu 36 suka jikkata,” in ji ta. Gwamnan Oaxaca, Salomon Jara, ya ce ya umarci hukumomi a jihar ta Kudu da su ba da tallafi ga waɗanda suka jikkata.

KU KUMA KARANTA: Aƙalla mutane 18 ne suka jikkata a Sri Lanka sakamakon hatsarin motar bas

“Muna aika ta’aziyya ga iyalan mamacin,” kamar yadda ya rubuta a shafukan sada zumunta.

Mummunan haɗurran tituna sun zama ruwan dare a Meziko, galibi saboda tsananin gudu, rashin yanayin abin hawa ko gajiyawar direba.

Irin waɗannan haɗarurrukan ne ke haddasa mace-mace tsakanin ‘yan ci-rani da ke tafiya mai hatsarin gaske zuwa Amurka.

A farkon watan Agusta, aƙalla mutane 18 ne suka mutu a lokacin da wata motar bas ɗauke da baƙin haure da ‘yan ƙasar Mexico suka kutsa cikin wani ƙwarin da ke jihar Nayarit da ke arewa maso yammacin ƙasar.

A watan Fabrairu, baƙin haure daga Venezuela, Colombia, da Amurka ta tsakiya sun yi hatsarin motar bas a tsakanin jihar Oaxaca da ke kudancin ƙasar da kuma tsakiyar Puebla wanda ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutane 17.

A watan Yuli, aƙalla mutane 29 ne suka mutu a lokacin da wata motar fasinja ta kutsa daga kan titin tsaunuka ta faɗa cikin wani rafi a Oaxaca.

A watan Disambar 2021, wata tirela ɗauke da baƙin haure 160 ta faɗa kan wata gadar masu tafiya a ƙafa a kan wata babbar hanya a jihar Chiapas da ke kudancin ƙasar, inda mutane 56 suka mutu, galibi ‘yan ƙasar Guatemala.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *