Mutane 13 sun mutu, 27 sun ɓace, sakamakon nutsewar wani jirgin ruwa a gaɓar tekun Tunisiya

0
123

Wani jami’in shari’ar ƙasar Tunisiya ya sanar a ranar Alhamis cewa an gano gawarwakin ‘yan ci-rani 13 ‘yan ƙasar Sudan, yayin da wasu 27 suka ɓace bayan wani jirgin ruwa ya nutse a ranar Laraba a gaɓar tekun Tunisiya bayan da ya taso daga Sfax. Mai shari’a Farid Ben Jha ya ce jirgin na ɗauke ne da mutane 42 dukkansu ‘yan ƙasar Sudan, sannan an samu ceto mutane biyu.

Ƙasar Italiya da wasu ‘yan Tunisiya da suka shiga ƙasar ta jirgin ruwa.

Tunisiya ta maye gurbin Libya a matsayin babbar hanyar da mutanen da ke gujewa talauci da tashe-tashen hankula a wasu wurare a Afirka da kuma gabas ta tsakiya ke samun ficewa daga arewacin Afirka da fatan samun ingantacciyar rayuwa idan suka isa Turai.

KU KUMA KARANTA:Dole kafafen watsa labarai su faɗi gaskiya idan ana son zaman lafiya a duniya – Altun

Ƙasar dai ta fuskanci yawaitar baƙin haure tun shekarar da ta gabata, inda ake yawan samun bala’o’i da suka haɗa da kwale-kwalen da ke nutsewa a gaɓar tekun ƙasar, yayin da suke ɗauke da baƙin haure daga yankin kudu da hamadar Saharar Afirka da fatan isa Italiya.

A shekarar 2023 jami’an tsaron gaɓar tekun Tunisiya sun gano gawarwakin baƙin haure kusan 1,000 da suka nutse a gaɓar tekun ƙasar, in ji jami’an ƙasar, wadda hakan shi ne fiye da na kowace shekara.

‘Yan Tunisiya ma na cikin waɗanda ke ƙoƙarin tsallakawa. Kimanin baƙin haure 40 ‘yan Tunisiya ne suka ɓace a watan da ya gabata bayan da suka tashi a cikin wani jirgin ruwa zuwa Italiya.

Leave a Reply