Muna ƙoƙarin kakkaɓe matsalar tsaro amma har yanzu ba mu yi nasara ba — Tinubu

0
146

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci shugabannin tsaro da su tabbatar da cewa an samu cikakkiyar nasara a kan ɗimbim matsalolin tsaro da ƙasar nan ke fuskanta.

Tinubu ya bayyana haka ne a jawabinsa ga hafsoshin tsaro da hukumomin leƙen asiri yayin taron ba da bayanai kan harkokin tsaro da aka gudanar ranar Juma’a a fadar gwamnati da ke Abuja.

Shugaba Tinubu ya ce yayin da ake samun ci gaba mai kyau tare da kawar da wasu matsalolin tsaro a wasu wuraren, a yanzu ba za a ayyana nasara ba har sai an kawo ƙarshen barazanar da ake fuskanta.

Ya bayyana cewa akwai buƙatar a ƙara jajircewa don tabbatar da magance matsalolin tsaron da ke ci wa ƙasar tuwo a ƙwarya.

KU KUMA KARANTA: An kafa wata rundunar tsaro ta musamman a jihar Filato

A yayin da yake gargaɗin cewa abin da ya faru a jihar Kaduna ba zai lamunci sake faruwar makamancinsa ba, Tinubu ya kuma yaba da haɗin kan da ake samu a tsakanin hukumomin tsaro a ƙasar.

“Nasarar da kuke samu abin a yaba ne. ‘Yan Najeriya na gani a ƙasa, amma ya kamata a yi ƙoƙarin kauce wa kura-kurai, irin wanda aka gani a baya-bayan nan a jihar Kaduna.

“Haƙiƙa haɗin kai da ake samu takanin jami’an tsaro na ƙara inganta a watannin baya-bayan nan, amma a yanzu ba lokacin nuna murna ba ne, har sai mun kakkaɓe matsalar baƙi ɗayanta,” in ji shugaba Tinubu.

Tinubun ya kuma ya buƙaci sojojin da su tabbatar da muradin ƙasar na haƙo ganga miliyan biyu na man fetur a kowace rana a cikin rubu’in farko na shekarar 2024.

Leave a Reply