Muna taya al’umman musulmai zagayowar watan azumin Ramadan — MƊD
“Ina mika sakon gaisuwa ta a daidai lokacin da al’ummar Musulmai da ke fadin duniya ke fara shirye-shiryen azumtar azumin watan Ramadan.
“Watan ramadan ya koyar da mu nuna halin kwarai na tausayawa, taimakekeniya karamci da kyawawan ɗabi’u da sauransu, sannan dama ce gare mu na ziyartar ‘yan uwa abokan arziki da ma sauran al’umma.
“Hakazalika dama ce na tunatar da mu wadanda ba su da ikon ganin watan.
“Saƙo na ga duk waɗanda suka samu damar ganin wannan lokaci mai tarin albarka, musamman ga waɗanda ke cikin halin gudun hijira ko tashin hankali, tabbas ina cikin damuwa matuka sakamakon wannan hali na iftila’i da kuke ciki ‘yan uwana.
KU KUMA KARANTA:Shugaban WHO ya tsallake rijiya da daya bayan harin da Isra’ila ta kai a filin jirgin Yemen
“Sannan, ina tare da ku a dukkan lokuta walau na tsanani ko na tashin hankali musamman ga wadanda yaki ya daidaita a Gaza da Sudan, da ma sauranan yankunan Sahel.
“Ina kira gare ku, da ku ba da hadin kai kamar yadda na bayar, don samun damar gudanar da azumin watan ramadan cikin kwanciyar hankali da lumana, kuma ina kira gare ku tare da neman goyon bayanku wajen zaman lafiya da mutunta juna.
“A ko wani ramadan, na kan kai ziyara ta haɗin kai, tare da yin azumi da al’ummar Musulmi a faɗin duniya.
“Wadannan ayyukan su na tunatar da duniya hakikanin halin kwarai na musulunci.
Hakanan a kodayaushe na kan samu kwarin gwiwa da kwanciyar hankali a wannan lokaci na ramadan.
“A cikin wannan wata mai alfarma, al’umma na samun daukaka ta hanyar haɓɓaka waɗannan kyawawan dabi’u, ya kamata mu rungumi juna don gina duniya mai cika adalci da zaman lafiya ga dukkan al’umma.
“Ina taya mu murnar zuwan wata mai alfarma ta ramadan.
“Ramadan Kareem”.