Muna son gwamnatin da za ta yi wa jama’a aiki ba kawai ta mulke su ba – Mazauna Abuja

0
34
Muna son gwamnatin da za ta yi wa jama’a aiki ba kawai ta mulke su ba – Mazauna Abuja

 

Muna son gwamnatin da za ta yi wa jama’a aiki ba kawai ta mulke su ba – Mazauna Abuja

Dubban jama’a na ci gaba da yin zanga zanga a kan tituna a Najeriya, a Abuja babban birnin tarayyar ƙasar masu zanga-zangar sun yi ta rera waƙoƙi yayin da suke guje wa barkonon tsohuwa da ‘yansanda suka harba.

A ranar Alhamis ne dai ‘yan Najeriya suka fara fitowa kan tituna suna neman a sauya wasu manufofin gwamnatin ƙasar, ciki har da cire tallafin man fetur da aka yi a shekarar da ta gabata.

Zanga zangar ta gama da za a yi tsawon kwanaki goma, an yi ta a biranen Najeriya da yawa, duk da arangamar da aka yi da jami’an tsaro a wasu wurare.

Ɗaya daga cikin masu zanga zangar, Wisdom Chimuanya, mazaunin Abuja ya ce, “Mun cancanci mu ci moriyar albarkatun da muke da su, muna da albarkatun ma’adinai, muna da albarkatun ƙasa, an albarkaci jama’a da abubuwa da yawa. Muna son gwamnatin da za ta yi wa jama’a aiki ba kawai ta mulke su ba, ya kamata shugaban kasa ya biya buƙatun jama’a, abin ya isa haka.”

A lokacin bikin rantsar da shi a watan Mayu, Shugaba Bola Tinubu ya sanar da kawo ƙarshen biyan tallafin man fetur. Ba a daɗe da hakan ba, shugaban ya kuma ɗauki matakin barin naira ta nema wa kanta daraja. Bayan haka, hukumomin ƙasar suka kuma kara kuɗin wutar lantarki da fiye da kashi 200.

Masu zanga-zangar sun ce wadannan manufofin sun sanya rayuwar yau da kullum zama da wahala.

KU KUMA KARANTA;Ɗaruruwan mutane sun fito zanga-zanga a birnin tarayya Abuja (Hotuna)

Da ta ke maida martani, rundunar ‘yan sandan kasar ta ce ta yi amfani da barkonon tsohuwa ne don wargaza masu zanga-zangar.

Benneth Igweh, shi ne kwamishinan ‘yan sanda na babban birnin tarayya, ya ce kotu ta ba da umurnin ne domin hana duk abin da zai kawo cikas ga al’amuran yau da kullum a kewayen birnin.

“Ba umarnina ba ne, ba umarnin sufeto janar na ‘yan sanda ba ne, ba umarnin kowa ba ne, umarnin kotu ne,” a cewar Igweh.

Kafofin yada labaran kasar dai sun ce an kashe mutane sha uku a fadin kasar a yayin zanga-zangar.

Hukumomi a jihohin Borno da kuma Kano sun sanya dokar hana fita a ranar Juma’a domin shawo kan tarzomar da aka yi a lokacin zanga zangar.

A watan da ya gabata, ‘yan majalisar dokokin Najeriya sun yi alkawarin ba da rabin albashinsu har tsawon wata shida ga ‘yan kasar, sannan hukumomi sun sassauta haraji kan wasu kayayyakin abinci da suka hada da alkama don rage farashinsu.

A ranar Litinin, Najeriya ta rattaɓa hannu a kan sabon mafi ƙarancin albashi. Sai dai masu zanga-zangar sun ce waɗannan matakan ba su wadatar ba, sun kuma sha alwashin mamaye tituna har sai an dawo da tallafin man fetur.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here