Muna neman afuwar al’ummar jihar Nasarawa – Rundunar sojin saman Najeriya

0
137

Daga Ibraheem El-Tafseer

Shugaban rundunar sojin saman Najeriya, Marshal Hassan Abubakar ya nemi gafarar gwamnatin da jama’ar jihar Nasarawa dangane da harin saman da suka kai wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama a ƙaramar hukumar Doma.

Abubakar wanda ya kai ziyarar ta’aziya ga gwamnan jihar, Abdullahi Sule yace ba da gangan jami’ansa suka kai harin ba a shekarar da ta gabata, saboda haka suna neman afuwar mutanen jihar.

Babban hafsan sojin saman yace sun samu bayanan asiri ne dangane da wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne a kan babura a kusa da ƙauyen Rukubi, a ƙoƙarin kai musu hari sai aka ritsa da fararen hular dake wurin.

Abubakar yace wannan dalili ne ya sa shi da manyan hafsoshin sa suka ziyarci jihar Nasarawa domin gabatar da ta’aziya da kuma neman gafarar mutanen jihar.

Babban hafsan sojin saman yace sun samu bayanan siriri ne dangane da wasu da ake zargin ‘yan ta’adda ne a kan babura a kusa da ƙauyen Rukubi, a ƙoƙarin kai musu hari sai aka ritsa da fararen hular dake wurin.

KU KUMA KARANTA: Sojojin Saman Najeriya ta halaka hatsabibin jagoran masu garkuwa da mutane, Janari, a Kaduna

Abubakar yace wannan dalili ne ya sa shi da manyan hafsoshin sa suka ziyarci jihar Nasarawa domin gabatar da ta’aziya da kuma neman gafarar mutanen jihar.

Babban hafsan wanda ya bayyana damuwa a kan matsalar tsaron da wasu sassan jihar ke fuskanta, ya sha alwashin ganin sun kawo ƙarshen matsalar garkuwa da mutane da ayyukan ta’addanci da satan shanu a Nasarawa da kuma Najeriya baki ɗaya.

Gwamnan jihar Nasarawa Abdullahi Sule ya yaba da matakin da sojin saman suka ɗauka na ɗaukar alhakin harin da kuma neman gafara.

Sule yace cikin waɗanda harin ya ritsa da su harda yaran wani dattijo mai shekaru 80 guda 9 da kuma shanunsa sama da 80.

Gwamnan yace lokacin da aka samu iftila’in ya rasa yadda zai tinkare ta, har sanda ya gayyaci shugabannin ƙungiyar Miyetti Allah ta Fulani makiyaya.

Sule yace lokacin da dattijon ya tambaye shi ko yaya zai yi bayan rasa yaransa guda 9 da shanunsa, sai jikinsa ya yi sanyi, inda ya roƙe shi ya mayar da al’amarin a matsayin ƙaddara.

Leave a Reply