Muna neman a bai wa jami’an mu iznin riƙe makamai a bakin aiki – Shugaban FRSC

0
242

Muna neman a bai wa jami’an mu iznin riƙe makamai a bakin aiki – Shugaban FRSC

Shugaban hukumar kiyaye haɗurra ta Nijeriya (FRSC), Shehu Mohammed, ya bayyana cewa bai ga wata hanya ta tabbatar da doka a titunan Najeriya ba face jami’ansa su samu izinin ɗaukar makamai.

Yayin da yake tattaunawa da gidan talabijin na ARISE a ranar Alhamis, Mohammed ya ce jami’an FRSC (Road Safety) na fuskantar barazana musamman idan suna tinkarar manyan motocin dakon kaya da ke ɗauke da fasinjoji sama da ƙima.

KU KUMA KARANTA: Gwamnan Kano ya umarci KAROTA, FRSC da su tilasta wa masu ababen hawa bin dokokin hanya

Jaridar Daily Trust ta ruwaito shi dangane da zargin cin hanci da wasu jami’an hukumar ke yi, Mohammed ya amince da hakan, amma ya jaddada cewa FRSC ta fi sauran hukumomi tsauri wajen hukunta jami’an da aka samu da laifi.

Leave a Reply