Muna neman ɗaukin Gwamnan Kano kan matsalar Taransifoma – Al’ummar Unguwar Bubbugaje

0
20
Muna neman ɗaukin Gwamnan Kano kan matsalar Taransifoma – Al’ummar Unguwar Bubbugaje

Muna neman ɗaukin Gwamnan Kano kan matsalar Taransifoma – Al’ummar Unguwar Bubbugaje

Daga Shafaatu Dauda Kano

Al’ummar unguwar Bubbugaje Gidan Jakada dake yankin ƙaramar hukumar Kumbotso ta jihar Kano, sun buƙaci gwamnan Kano, Injiniya Abba Kabir Yusif, ya kawo musu ɗauki akan matsalar Na’urar Taransifomar su wadda take neman sabauta rayuwar su.

Al’ummar unguwar sun bayyana hakan ne a yayin zantawar su da jaridar Neptune prime Hausa, inda suka ce kimanin shekaru 3 suna cikin halin duhun duƙununu a sakamakon rashin wutar lantarkin.

Yayin Zanta war Jaridar Neptune prime da shugaban kwamitin fafutikar neman Tiransifomar, Malam Sani Nasidi Uba, ya ce abin yana ci musu tuwo a ƙwarya la’akari da yadda dukkan unguwannin dake zagaye dasu suke kwana da wuta, amma su rashin Transifomar ya maida unguwar tasu tamkar wani Kabari na nan duniya.

A cewarsa, “Muna cikin mawuyacin hali a tsawon waɗannan shekaru duba da yadda Transifomar tamu take yin bindiga da zarar an gyara ta a sakamakon lodin da ya yi mata yawa, mafari kenan da masana suka tabbatar da sai dai a samar mana Tiransomar me ƙarfin K V I 5000“.

KU KUMA KARANTA:Ina neman diyyar mahaifina – Ɗan Mai Tsaron Sarkin Kano Sanusi da aka kashe

Haka kuma ya ƙara da cewa matsalar ta haifar musu da matsaloli da dama a unguwar kamar tsadar rayuwa, matsalar tsaro, ƙaruwar cututtuka da dai sauran waɗanda ba za’a iya faɗar su a kafafen yaɗa labarai ba.

Isyaku Abdulmalik shine mai unguwar Bubbugaje ya ce sunje duk inda ya kamata suje domin isar da koken su, amma an gaza share musu hawayen su dangane da matsalar rashin wutar lantarkin isyaku ya jaddada kiran su ga gwamnan Kano da ya kawo musu ɗauki.

A ƙarshe sunyi fatan dukkan masu ruwa da tsaki dasu kawo musu ɗauki domin ya zama sun fidda su daga halin ƙuncin da suke ciki har na tsawon shekaru Uku a sakamakon lalacewar Na’urar Transifomar.

Leave a Reply