Muna iya ƙoƙarinmu wajen samar da zaman lafiya da tsaro a jihar Yobe – Gwamna Buni

0
108

Daga Ibraheem El-Tafseer

Gwamnan Jihar Yobe, Hon. Alhaji Mai Mala Buni ya ba da tabbacin goyon bayan gwamnatinsa ga jami’an tsaro a jihar domin inganta aikin sintiri akan iyakokin ƙasa.

Buni ya bayar da wannan tabbacin ne a ranar Alhamis, a lokacin da ya karɓi baƙuncin mataimakin shugaban hukumar shige da fice ta shiyyar C, Sunday James, wanda ya kai masa ziyarar ban girma a gidan gwamnati da ke Damaturu.

Gwamnan ya bayyana ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da ɗorewar zaman lafiya da tsaro a jihar.

Ya yabawa jami’an tsaro bisa jajircewarsu wajen daƙile ta’addanci da miyagun laifuka gaba ɗaya a yankin arewa maso gabas.

Gwamnan ya yi ƙira ga hukumomin da su yi aiki tare, haɗe da ɗaukar aikin sintiri na haɗin gwiwa don duba yadda masu aikata laifuka ke kutsawa cikin jihohin kan iyaka.

Ya kuma yi ƙira ga jami’an tsaro da su haɗa kai da shugabannin gargajiya da na al’umma domin gano wurare da masu aikata laifuka cikin sauƙi.

Tun da farko, mai kula da shiyyar Sunday James ya yabawa Gwamna Buni bisa yadda yake tallafawa jami’an tsaro wajen yaƙi da miyagun laifuka.

“Mai girma gwamna, na gamsu da irin goyon bayan da gwamnatinka ke bayarwa, wanda ya haifar da ƙaruwar zaman lafiya da tsaro a faɗin jihar nan.

“Nasarar da aka samu a yaƙin da ake yi da masu tayar da ƙayar baya da kuma aikata laifuka gaba ɗaya ba ta yiwuwa ne kawai ta hanyar goyon bayan ku,” in ji ACG.

Leave a Reply