Muna ganin ribar ƙin yin sulhu da ‘yan bindiga – Gwamna Dauda Lawal

0
19
Muna ganin ribar ƙin yin sulhu da ‘yan bindiga – Gwamna Dauda Lawal

Muna ganin ribar ƙin yin sulhu da ‘yan bindiga – Gwamna Dauda Lawal

Gwamnanatin jihar Zamfara ta ce kwalliya na biyan kudin sabulu a matakin da ta dauka na kin yin sulhu da barayin daji.

Gwamnan jihar Dauda Lawal ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito yayin da ya karbi bakuncin Babban Hafsan Sojin Saman Najeriya, Air Marshal Hassan Bala Abubakar.

Abubakar ya kai wa gwamnan ziyara domin yin jaje kan kuskuren jefa bama-bamai akan fararen hula da dakarun “Operation Fansan Yamma” suka yi.

KU KUMA KARANTA:Da ilimi ake samun kowace irin nasara a rayuwa – Dauda Lawal 

A cewar Lawal, zaman lafiya na dawowa a hankali a jihar ta Zamfara da ke yammacin arewacin Najeriya wacce ta jima tana fama da hare-haren barayin daji.

A ranar 11 ga watan Janairun 2025, wasu hare-haren sama da dakarun Najeriya suka kai a Gidan Makera da ke jihar Maradun suka hallaka wasu fararen hula su 11.

Dakarun na Najeriya n kokarin kawar da gungun barayin daji da ke kai hare-hare karkashin jagorancin Bello Turji wanda ya addabi wasu ynkunan jihar.

Leave a Reply