Muna da ƙwarin guiwar samun nasara kan Isra’ila – Hezbollah
Daga Ibraheem El-Tafseer
A cikin wata sabuwar sanarwa da ta fitar kan cikar harin da Hamas ta kai Isra’ila shekara guda, Hezbollah ta ce tana da ƙwarin guiwar samun nasara a yaƙinta da Isra’ila, inda ta ce za ta ci gaba da gwabzawa da Isra’ilar.
Iran ce ke ɗaukar nauyiin Ƙungiyoyin Hezbollah da ke da mazauni a Lebanon da kuma Hamas.
Hezbollah ta bayyana harin da Hamas ɗin ta kai da na jarumtaka wanda tarihi ba zai manta da shi ba a yankin.
KU KUMA KARANTA: Ƙasar Iran ta karrama kwamandan da ya kai wa Isra’ila hari
“Ba wajen zaman Isra’ila ba ne, saboda haka dole mu kawar da ta duk tsawon lokacin da za a ɗauka”
Hezbollah ta kuma ɗora alhakin yakin Gaza da Lebanon kan Amurka da ƙawayenta.