Muna cikin fargabar rasa gidajenmu – mazauna unguwar Kwari Potiskum

0
382

Daga Ibraheem El-Tafseer

Al’ummar da suke zaune a unguwannin Kwari, Batayya da Kusa da Gadar hanyar Kano dake garin Potiskum jihar Yobe, sun koka a kan yadda suke fuskantar barazanar ruwan sama na zabtarewa haɗe da rushewar gidajensu. Jama’ar wannan yanki sun shafe shekara da shekaru ruwan yana musu barazana, wasu kuma tuni har sun tashi sun bar muhallan nasu, sakamakon ruwan ya cinye gidajen nasu gabaɗaya.

Waɗanda wannan barazanar zabtarewar gidajen ya fi shafa, sune waɗanda gidajen su yake kusa da hanyar da ruwan yake wucewa. Duk lokacin da ake ruwan sama, to su fa al’ummar wannan unguwannin hankalinsu ba a kwance yake ba. Wasu ma tashi suke su bar unguwar, sai an gama ruwan sannan su dawo.

Wakilinmu ya shiga unguwar, kuma ya gane wa idonsa yadda ruwan yake musu barazana. A tattaunawar da ya yi da wasu daga cikin mazauna unguwar sun shaida masa cewa, sun kai kukansu wajen gwamnatin jihar Yobe, ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba. Amma har yanzu gwamnati ba ta waiwayo su ba. Suka ce duk shekara ruwan sai ya cinye gidajen jama’a, sakamakon rashin gyara da gwamnatin ba ta yi ba a hanyar da ruwan yake wucewa.

“Gwamnatin Alhaji Mai Mala Buni, mun je mun koka mata a kan wannan matsala da muke fuskanta na rasa gidajenmu sakamakon rashin gyara a wannan hanyar ruwa, zuwa yanzu dai ba mu ga komai ba. Amma muna zuba ido” inji wani mazaunin unguwar, Malam Salihu Muhammad.

Malam Abbas Hassan, wani mazaunin unguwar ne, kuma wanda wannan zabtarewar gidajen yake masa barazana, ya shaida wa Neptune Hausa cewa “wannan damuna ta bana ina cikin fargaba da matsanancin tashin hankali, domin bai fi saura mita takwas ruwan ya cinye gidana ba. Idan kuma ruwa ya raba ni da gidan nan, to fa ban san inda za mu shiga ni da iyalaina ba. Muna fatan kukanmu zai kai ga kunnen gwamnati” cikin alhini da ban tausayi yake koka wa gwamnatin jihar Yobe halin da suke ciki.

Leave a Reply