Muna ƙira ga gwamnatin Kano da ta samar mana da Asibiti – Al’ummar Unguwar Magashi
Daga Jamilu Lawan Yakasai
Al’ummar unguwar ta magashi sun koka kan rashin asibiti a wannan yankin.
Sun ce sakamakon rashin asibiti hakan yasa sukan shan wahala matuka a ya yin da rashin lafiya ta kama mutum.
Hakan na sanya wasu lokunta ayi asarar rai kafin fita zuwa manyan asibitoci, wanda sukace sabida yawan al’ummar da suke zuwa manyan asibitoci musamman asibitin Murtala Muhammad, wanda shine mafi kusa dasu,
Matsalar kafin mutum yafito yazo asibitin ya jigata matuka, sannan idan anzo manyan asibito kafin a duba mutum sai anyi zurga-zurgar neman katin gannin likita, wanda shi kanshi wajen karbar katin sai anbi layi mai tsayi, wanda take kaiwa mutum ya jikkata sosai kafin akarbi kati.
KU KUMA KARANTA:An sace wata dattijuwa a asibitin Dawanau dake Kano
Sannan daga bisani a zo aga likita a cewar al’ummar yankin.
Inda suka ce, koda karamin asibitin “Sha ka tafi” ne a samar musu sakamakon yawan da al’ummar wannan unguwa ke ciki.
Daga karshe sunyi fatan wannan koke nasu zaije ga idanun mahukunta, domin kai musu agajin gaggawa