Muna ƙira da a tallafa wa ci gaban matasa – Gwamnatin Tarayya (Hotuna)

0
27
Muna ƙira da a tallafa wa ci gaban matasa - Gwamnatin Tarayya (Hotuna)

Muna ƙira da a tallafa wa ci gaban matasa – Gwamnatin Tarayya (Hotuna)

Gwamnatin Tarayya ta yi ƙira ga masu-ruwa-da-tsaki a matakai daban-daban da su shigo a dama da su wajen inganta rayukan matasa don su samu gobe mai kyau.

Ƙaramin Ministan Ci-gaban Matasa, Ayodele Olawande, ya gabatar da jawabin, a lokacin taron taya Majalisar Ɗinkin Duniya cikar ta shekaru 79 da samar da ita.

Ministan ya ce, Najeriya ta na ɗaya daga ƙasashen da ke da tarin matasa masu yawa inda kusan kaso 70 na waɗanda ba su haura shekaru 35 ba ne da ke da zimmar kawo sauyi a ɓangarori daban-daban na rayuwa da za su samar da ci-gaba.

Duk da ƙalubalen da tattalin arziƙin Najeriya ke fuskanta, Ministan ya ce gwamnati da haɗin-gwiwar MƊD tare da masu ƙoƙarin kawo sauyi mai amfani ga al’umma su na aiki tuƙuru wajen samar da hanyoyin samun inganta ƙirƙira acikin matasa.

KU KUMA KARANTA: MƊD ta yi alƙawarin tallafa wa Najeriya wajen cimma burin SDG (Hotuna)

Ministan ya ƙara da cewa, wajibi ne sai matasa sun samu ilimi mai nagarta da damammakin ayyuka, don haka ya ke fatan a samu tsari da zai fifita matasa da damawa da su cikin ababen da za su haifar musu da gobe mai kyau.

A lokacin da ya ke jawabi a taron, wakilin Jin-ƙai na MƊD a Najeriya, Mohamed M. Malick, ya yaba wa gwamnatin ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu wajen samar da tsare-tsare sama da talatin daga MƊD don su yi aiki a Najeriya, ya na mai tabbatar da cewa za su cigaba da bai wa ƴan Najeriya tallafi a kowane ɓangare da ƙasar ta sa a gaba wajen inganta rayukansu.

Ya kuma tabbatar da cewa, su na fatan a cimma burace-buracen cigaba na SDG a Najeriya zuwa nan da shekara ta 2030 kamar yadda aka tsara.

Cikin ababen da SDG ya zayyano don kawo ci-gaba mai ɗorewa a ƙasar akwai batun samar da ilimi mai nagarta, kawo ƙarshen talauci, fuskantar sauyin yanayi da yaƙar cutuka da makamantansu.

Kalli hotunan a nan:

Leave a Reply