Mun kashe ’yan boko haram 5, 44 sun miƙa wuya – Sojojin Najeriya
Daga Ali Sanni Larabawa
Rundunar Sojin Najeriya, ta sanar da cewar dakarunta sun kashe ’yan ta’adda biyar tare da kama wasu 44 da suka miƙa wuya a jihar Borno.
Wannan na ɗauke ne a cikin wata sanarwa da rundunar sojin ta fitar a shafinta na X (twitter), a ranar Talata.
A yayin ayyukansu, sojojin sun gano abubuwa masu fashewa, makamai, alburusai, da shanun da aka sace, sannan sun kama wasu masu laifi.
Sojojin, sun bayyana cewa a ranar Litinin, sun kai hari sansanin ’yan ta’addan ISWAP da ke yankin Bama a jihar Borno.
KU KUMA KARANTA: Mayaƙan ‘Boko Haram’ a Borno sun kashe ɗan sanda da ƙona motocin sintiri
A wannan samamen, sun kashe ’yan ta’adda biyar tare da ƙwato wasu abubuwa kamar bam, RPG, bindigogi guda biyu, AK-47, alburusai 23, babura guda shida, da kuma wasu magunguna.
Kazalika, sojojin sun ce sakamakon ci gabada kai hare-hare a yankin Arewa Maso Gabas, ’yan Boko Haram guda 44 da iyalansu sun miƙa wuya ga dakarun a yankunan Bama, Dikwa, da Gwoza na jihar ta Borno.