Mun ba wa Gwamnan Neja wa’adin awa 48 ya janye dakatarwar da ya yiwa gidan rediyon Bategi – Ƙungiyar ‘Yan Jaridu ta Duniya
Daga Jameel Lawan Yakasai
Kungiyar ’Yan Jarida ta Duniya ‘International Press Institute’ (IPI) reshen Najeriya ta bai wa Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, wa’adin sa’o’i 48 da ya janye umarnin rufe gidan rediyon Bategi FM da ke Minna, wanda ya bayar yayin wani taron jam’iyyar APC.
A cikin wata sanarwa da shugabanta, Musikilu Mojeed, da mai ba da shawara kan harkokin shari’a, Tobi Soniyi, suka rattaba hannu, kungiyar ta bayyana matakin a matsayin keta ‘yancin fadar albarkacin baki da ‘yancin kafafen yada labarai, tare da siffanta shi a matsayin barazana ga dimokuradiyya.
KU KUMA KARANTA: NBC ce ke da hurumin dakatar da Bategi FM ba Gwamnatin Neja ba – Minista
IPI ta tunatar da gwamnan cewa matakin nasa ya saba da sashe na 22 da 39 na Kundin Tsarin Mulkin Najeriya, kuma ta bukaci a soke dakatarwar ba tare da wani sharadi ba, in ba haka ba za ta dauki karin matakai. Ta ce irin wannan rufe kafafen yada labarai na cutar da al’umma ta fuskar samun bayanai da bayyana ra’ayoyi.









