No menu items!

Sample Page Title

Date:

A wani samame na sahihanci da suka kai kan ‘yan ta’addan da ke jihar Sakkwato, sojojin runduna ta 8 ta Garrison sun tarwatsa ‘yan bindigan a ƙauyen Tukandu, inda suka watse gungun ‘yan ta’adda da suka  yi ƙaurin suna wajen aikata munanan ayyuka a yankin baki ɗaya.

Jami’in  hulɗa da jama’a na rundunar, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, ya ce sojojin sun yi aikin ne a ranar Talata, 24 ga watan Oktoba, 2023.

“Mummunan harin da sojojin suka kai ya kawo ƙarshen ‘yan ta’adda da dama, yayin da wasu suka gudu da raunukan harbin bindiga. A wani samame da sojojin suka kai sun ƙwato bindigu ƙirar AK-47 guda uku, Bindigar PKT ɗaya, harsashi na musamman 125, 7.62, roka 2 da bama-bamai da kuma babura guda 9.”  Inji shi.

“Shugaban hafsan soji, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ya yaba wa sojojin, inda ya buƙace su da su jajirce tare da ci gaba da zafafa kai hare-hare kan ‘yan ta’addan domin murƙushe su tare da hana su ‘yancin ɗaukar mataki.”

Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman Abubakar
Maryam Sulaiman, ƙwararriyar ‘yar jarida ce mai kishin ƙasa, wacce ta sadaukar da kanta wajen kawo sauyi a cikin al’umma ta hanyar fahimta da daidaita rahotanni.

Leave a Reply

Share post:

Subscribe

Popular

More like this
Related

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin Tinubu na janyewa daga gadin manyan mutane

Sojoji sun kama wasu ’yansanda bisa ƙin bin umarnin...

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a Saudiyya 

Tsohon shugaban Alƙalan Najeriya, Ibrahim Tanko, ya rasu a...

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano

Matashi ya yanke maƙogwaron ladanin wani masallaci a Kano Daga...