Mugun mafarki ya ingiza matashi buga wa mahaifinsa taɓarya a Kaduna

0
213

‘Yan sanda a jihar Kaduna sun ce sun kama wani matashi mai shekara 20, bisa zargin kashe mahaifinsa ta hanyar buga masa taɓarya bayan zuciyarsa ta ƙaddara masa cewa uban na yunƙurin halaka shi.

“Ya shaida mana cewa yana yin mafarke-mafarke, inda yake ganin siffar mahaifin nasa, mai kimanin shekara 50, yana zuwar masa a cikin sigar jemage,” in ji mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar.

ASP Mansur Hassan ya shaida wa manema labarai cewa suna ci gaba da gudanar da bincike kan matashin da suke zargi wanda ya fito daga yankin ƙaramar hukumar Zangon Kataf.

KU KUMA KARANTA: Uwargida ta kwaɗa wa maigida taɓarya a kai, ya mutu har lahira

Ya ce zuwa yanzu ba su samu wata shaida da ke nuna cewa matashin na da wata matsalar kwakwalwa, ko kuma yana shan kayan maye.

Jami’in ‘yan sandan ya ambato matashin na cewa babu kyakkyawar alaƙa tsakaninsa da mahaifin, wanda ya riga mu gidan gaskiya.

‘Yan sandan sun ce da zarar sun kammala bincike za su gurfanar da matashin mai suna David Phillips a gaban kotu.

Leave a Reply