Daga Ibraheem El-Tafseer
Kamfanin sadarwa na MTN a Najeriya ya nemi afuwar aboka hulɗar sa sakamakon matsalar ɗaukewar sabis da kamfanin ya fuskanta a faɗin ƙasar.
Tun da tsakar ranar Laraba ne dai masu amfani da layin MTN suka fara fuskantar matsalar ɗaukewar sabis a layukansu.
KU KUMA KARANTA: Kamfanonin sadarwa na MTN, Glo da Airtel za su ƙara kuɗin data
To sai dai kamfanin cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, ya ce hakan ya faru ne sakamakon yankewar wasu wayoyin sadarwar kamfanin, lamarin ya ya shafi ƙira da kuma fannin intanet a layin.
Kamfanin ya kuma ce injiniyoyinsa na aiki domin shawo kan matsalar, inda ya ce sannu a hankali sabis ɗin ya fara dawowa a wasu yankuna.