Motocin kayan agaji sun fara shiga zirin Gaza

0
164

A safiyar ranar Asabar, motoci 20 daga cikin motoci sama da 200 suka fara shiga ta iyakar Zirin Gaza na Rafah da ke ƙarƙashin kulawar ƙasar Masar.

Jerin gwanon manyan motoci ɗauke da kayan abinci da magunguna da sauran kayan agaji sun fara shiga Zirin Gaza daga ƙasar Masar.

Rukunin farko na motocin suna ɗauke da kayan jinƙai ne daga ƙungiyar agaji ta Red Crescsent, wadda ta bayyana cewa yawan kayan da aka shiga bai kai cikin cokalin abin da ake bukata a Gaza ba.

Motocin sun samu izinin tsallakawa zuwa Zirin Gaza ne bayan da suka shafe kwanaki suna jiran sahalewar hukumomin ƙasar Masar.

Tun ranar 7 ga watan Oktoba, 2023 Masar ta datse mashigar tun bayan ɓarkewar sabon faɗa tsakanin Isra’ila da ƙungiyar Falasɗinawa ta Hamas a ranar Asabar da ta gabata.

A ranar Juma’a Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, Antonio Gutteres, ya ziyarci Masar domin ganin shirye-shiryen shigar da kayan agajin ta hannun Red Crescent.

KU KUMA KARANTA: Isra’ila ta kai hari a kan wani Coci a Gaza, ta kashe mutane da dama

Masar ta amince a shigar da kayan agajin Gaza ne bayan tattaunawa da Shugaban Amurka, Joe Biden; matakin da Isra’ila ba ta amince ba, da cewa babu kayan tallafin da zai isa ga Hamas.

Hukumomin Gaza sun bayyana cewa kawo yanzu Falasɗinawan da Isra’ila sun kai 4,135, tare da jikkata wasu sama da 13,000.

Hakan na zuwa ne bayan Hamas ta sako wasu Amurkawa biyu (uwa da ’yarta) daga cikin mutanen da ƙungiyar ta yi garkuwa da su.

Leave a Reply